Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin MDD A Liberiya Yace Ana Bukatar Sojoji Dubu 15 A Kasar - 2003-09-06


Wakilin MDD na musamman a Liberiya, ya ce ana bukatar sojoji dubu 15 domin tabbatar da kwanciyar hankali a wannan kasa da yaki yayi wa illa a Afirka ta Yamma.

Jacques Klein ya shaidawa 'yan jarida jiya Jumma'a a Monrovia, babban birnin Liberiya, cewar a mako mai zuwa zai roki Kwamitin Sulhun majalisar da ya ba da iznin tura wadannan sojoji.

Mr. Klein ya ce za a ci gaba da kashe-kashe da fyade da kwasar ganima da musugunawa jama'a a Liberiya idan har ba a girka sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD masu yawa a kasar ba.

Idan har aka amince da shawarar da Mr. Klein zai gabatar, sojojin kiyaye zaman lafiyar na MDD zasu maye gurbin sojoji kimanin dubu biyu na Afirka ta Yamma da Nijeriya take yi wa jagoranci, wadanda akasarinsu suna babban birnin kasar ne.

A cikin wannan mako, sai da wasu sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yammar suka yi tattaki zuwa arewa da Monrovia domin binciken rahotannin da aka samu na barkewar fada.

Amma kuma wani kakakinsu ya ce ba su gani, ko kuma ji wani abu da ya gaskata rahotannin fadar ba.

XS
SM
MD
LG