Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun MDD Ya Duba Daftarin Kudurin  Da Amurka Ta Zana Kan Iraqi - 2003-09-06


Kwamitin Sulhun MDD ya kammala zaman farko a asirce na tuntubar juna kan kudurin da Amurka take son a zartas game da kasar Iraqi.

A bayan tattaunawar da aka yi jiya Jumma'a a New York, jakadan Britaniya Emyr Jones Parry, ya ce wakilai 15 na Kwamitin Sulhun sun yarda a kan bukatar dake akwai ta kara rawar da MDD zata taka a Iraqi. Ya ce wakilan Kwamitin sun bayyana ra'ayoyinsu a game da kudurin na Amurka suka kuma yarda cewar akwai bukatar karfafa rawar da MDD zata taka a fagen siyasar Iraqi.

Kudurin na Amurka yayi kira ga Kwamitin Sulhu da ya zana lokacin da a kirkirowa da Iraqi sabon tsarin mulki tare da gudanar da zabubbuka. Har ila yau kudurin zai bayar da iznin kafa rundunar kasa da kasa wadda za a sanya karkashin jagorancin Amurka domin maido da kwanciyar hankali a Iraqi.

Sai dai kuma wasu wakilai uku na Kwamitin Sulhun, Rasha da Faransa da kuma Jamus, sun bayyana damuwa kan wannan kudurin da Amurka ta zana. Jamus ta ce tana son a bai wa MDD rawa sosai, yayin da Faransa ta ce tilas ne a bai wa majalisar karin ikon fada a ji game da makomar siyasar Iraqi.

XS
SM
MD
LG