Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arafat Ya Bukaci Kakakin Majalisar Dokoki Ya Zamo Sabon Firayim Ministan Falasdinawa - 2003-09-08


Jami'an Falasdinawa sun ce Yasser Arafat ya bukaci kakakin majalisar dokoki, Ahmed Korei, ya zamo sabon firayim ministansa.

Suka ce wasu muhimman kwamitoci guda biyu na Falasdinawa sun amince da nadin Malam Korei a jiya lahadi. A ranar asabar, firayim ministan Falasdinawa Mahmoud Abbas, yayi murabus, a bayan da aka ce ya kasa daidaitawa da Malam Arafat kan ikon bayar da umurni ga dakarun tsaron Falasdinawa.

Sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell, ya ce kokarin wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai cije sai fa idan firayim ministan na Falasdinawa yana da cikakken iko a kan dakarun tsaro. Isra'ila da Amurka ma sun ce ba zasu yi hulda da duk wata gwamnatin Falasdinawan da Malam Arafat ko masu yi masa biyayya suke gudanarwa ba.

A halin da ake ciki, jami'an tsaron Falasdinawa sun ce wata helkwaftar kai farmaki ta Isra'ila ta cilla makamai masu linzami akalla uku a kan gidan wani dan kungiyar Hamas a Gaza. Suka ce mutane akalla goma suka ji rauni a wannan hari na jiya lahadi da maraice.

Jami'an Isra'ila suka ce Hamas tana yin amfani da gidan wajen tara nakiya. Tun da fari a jiya lahadin, firayim ministan Isra'ila Ariel Sharon, ya ce sun yanke shawarar za su kashe dukkan shugabannin Hamas. A ranar asabar, Isra'ila ta kai wani harin da ya ci tura inda ta nemi kashe shugaban addini na Hamas, Sheikh Ahmed Yassin.

Hamas ta yi kashedin cewa Isra'ila ta "bude kofofin jahannama" da ta kai wannan harin, kuma zata mayar da martanin da Isra'ila ba ta taba ganin irinsa ba.

XS
SM
MD
LG