Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yayi Alkawarin Daukar Kowane Irin matakin Da Ake Bukata Domin Murkushe Ta'addanci - 2003-09-08


Shugaba Bush yayi alkawarin daukar kowane irin matakin da ake bukata domin samun nasara a yakin da ake yi da ta'addanci a fadin duniya, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su taimaka a Iraqi, yayin da ya nemi majalisar dokokin Amurka ta ba shi dubban miliyoyin daloli.

A cikin jawabin da yayi ga Amurkawa ta telebijin cikin daren lahadi, Mr. Bush ya ce zai dauki duk wani matakin da ake bukata, zai kuma kashe duk kudin da ake bukata domin samun nasarar yaki da ta'addanci tare da tabbatar da tsaron Amurka.

Mr. Bush ya ce yana shirin tambayar majalisar dokoki da ta ba shi dala miliyan dubu tamanin da bakwai domin biyan kudin ayyukan soja tare da sake hgina kasa a Iraqi da Afghanistan.

Shugaban ya ce a yanzu wakilan majalisar dinkin duniya suna da dama da kuma nauyin kara irin rawar da suke takawa a Iraqi.

XS
SM
MD
LG