Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Watakila Nan Da Nuwamba Za A Girka Karin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya A Liberiya - 2003-09-12


Wani babban jami'i mai bai wa MDD shawara kan harkokin soja, ya ce yana fatan ganin an girka sojojin kiyaye zaman lafiya su dubu 15 a kasar Liberiya nan da tsakiyar watan Nuwamba.

Babban mai bayar da shawara kan harkokin soja ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, Manjo janar Patrick Cammaert, shi ya furta wannan jiya alhamis.

Ya ce kasashen duniya suna bayar da martani na yin na'am da kiran da aka yi na karin sojojin da za su yi aiki a rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD da za a girka a wannan kasa da yaki ya lalata a Afirka ta Yamma.

A makon da ya shige, wakilin MDD na musamman a Liberiya, Jacques Klein, ya ce zai nemi Kwamitin Sulhun majalisar da ya amince da tura sojojin da za su tabbatar da yin aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla kwanakin baya a tsakanin gwamnatin Liberiya da 'yan tawayen kasar.

Rundunar tana iya hadawa da sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma wadanda Nijeriya take yi musu jagoranci yanzu haka a kasar Liberiya. Ya ce Indiya da Pakistan suna daga cikin wadanda watakila za su tura sojojinsu.

XS
SM
MD
LG