Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Amince Da Dage Takunkumin Da MDD Ta kakabawa Libya - 2003-09-12


Ministan harkokin wajen Faransa, Dominique de Villepin, ya ce a yanzu dai Faransa ba ta yin adawa da kuri'ar da aka shirya Kwamitin Sulhun MDD zai jefa yau Jumma'a kan dage takunkumin da aka sanyawa Libya.

A jiya alhamis Libya ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar biyan diyya ga iyalan mutane 170 da suka mutu a lokacin da bam ya tarwatsa wani jirgin saman fasinja na Faransa a saman jamhuriyar Nijar a 1989.

Wani kakakin iyalan ya ce za a tattauna a kan yawan karin da za a yi wa iyalan kafin a rattaba hannu kan kammalalliyar yarjejeniya a cikin wata guda.

A baya, Faransa ta yi barazanar hawa kujerar-na-ki domin hana dage takunkumin. Ta bukaci da a kara yawan diyyar da za a biya iyalan wadanda suka mutu a jirgin na Faransa, a bayan da Libya ta yarda za ta biya iyalan wadanda suka mutu a jirgin Amurka da ya fado kan garin Lockerbie dubban miliyoyin daloli.

Faransa ta bayyana matakin nata a zaman yunkurin tabbatar da cewa an yi adalaci ga kowa da kowa.

XS
SM
MD
LG