Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Zartaswar Tsaron Bani Isra'ila ta Yanke Shawarar Korar Shugaban Falasdinawa Yasser Arafat - 2003-09-12


Majalisar zartaswar tsaron Isra'ila ta yanke shawarar amincewa da manufar korar shugaban Falasdinawa daga yankin, amma kuma ta ce ba zata yi hakan nan take ba.

Majalisar zartaswar tsaron ta ce Malam Arafat yana kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, ta kuma bukaci rundunar sojan Isra'ila da ta tsara shirin korarsa daga yankunan Falasdinawa.

Amma kuma Malam Arafat ya ce ba zai kyale Isra'ila ta kore shi zuwa gudun hijira ba, kuma ya fito waje na dan gajeren lokaci a bayan da dubban magoya baya suka yi tsinke wa gidansa a Ramallah.

A bayan da Isra'ila ta bayar da wannan sanarwa, sabon firayim ministan Falasdinawa, Ahmed Korei, yayi barazanar dage kokarin da yake yi na kafa sabuwar gwamnati.

Amurka ta ce korar malam Arafat ba zata taimakawa shirin samar da zaman lafiyar ba.

XS
SM
MD
LG