Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwa Ya Cinye Somaliya 'Yan Gudun Hijira A Kusa Da Yemen - 2003-09-14


Jami'an kasar Yemen da na Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD, sun ce mutane akalla 18 sun mutu, akasarinsu Somaliyawa, a lokacin da aka tilasta musu fadawa ciklin teku a daidai lokacin da kwale-kwalen da suke ciki yayi kusa da gabar kasar Yemen.

Jami'an suka ce an ceto 'yan gudun hijira 55, amma har yanzu akwai 27 da suka bace ba a san inda suke ba.

Wadanda suka kubuta da rayukansu, akasarinsu Somaliya da 'yan ethiopia, sun ce ma'aikatan jirgin suka auna su da bindigogi suka ce ko dai su fada cikin ruwa, ko su harbe su.

Wasu Somaliya da 'yan Ethiopia sun taba bayar da irin wannan labarin a watan Agusta.

Hukumar Kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce a lokuta da dama, matuka jiragen ruwa su kan tilasta wa bakin haure fadawa cikin teku, domin gujewa cin karo da jiragen ruwan sintirin teku na Yemen.

XS
SM
MD
LG