Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Amince Da Girka Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Dubu 15 A Liberiya - 2003-09-20


Ba tare da hamayya ba, Kwamitin Sulhun MDD ya aince da tura sojojin kiyaye zaman lafiyar da yawansu zai iya kaiwa dubu 15 a kasar Liberiya, domin sanya idanu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da taimakawa wajen sake gina kasar a bayan yakin basasar shekaru 14 kusan babu tsayawa.

Wannan kudurin da Amurka ta zana aka kuma amince da shi jiya Jumma'a, ya bayar da izni ga rundunar ta MDD ta karbi ayyukan kiyaye zaman lafiya daga hannun wata rundunar Afirka ta Yamma a ranar 1 ga watan Oktoba. Za a shigar da wadannan sojoji dubu 3 da 500 na Afirka ta Yamma da Nijeriya take yi wa jagoranci a cikin rundunar ta MDD.

Shugaban Kwamitin Sulhu mai ci, Emyr Jones Parry na Britaniya, ya bayyana kudurin na Liberiya a zaman shaidar aniyar majalisar ta tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Afirka.

Ana sa ran cewa rundunar ta Liberiya zata kunshi sojoji daga kasashen Pakistan, bangladesh, Afirka ta Kudu, Ethiopia, Namibiya, Rasha da Ireland, a bayan na kasashen Afirka ta Yamma dake can a yanzu.

XS
SM
MD
LG