Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Zauren MDD Ya Bukaci Isra'ila Da Ta Janye Barazanar Da Ta Yi Wa Arafat - 2003-09-20


Babban zauren taron MDD ya zartas da wani kuduri wanda ya bukaci Isra'ila da ta janye barazanar da ta yi ta kora ko kuma kashe shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat.

Kasashen Larabawa suka yi kiran da a jefa kuri'a kan wannan kuduri jiya Jumma'a, a bayan da Amurka ta hau kujerar-na-ki ta toshe kafar zartas da kuduri makamancin wannan ranar talata a Kwamitin Sulhun MDD.

Kudurin na karshe da aka zartas ya kunshi gyare-gyaren da suka yi tur da hare-haren kunar bakin wake da Falasdinawa ke kaiwa da kuma farautowa domin kashe 'yan kishin Falasdinu da Isra'ila take yi.

Kasashe 133 suka jefa kuri'ar amincewa da kudurin, guda hudu kawai suka ki yarda, yayin da kasashe 15 suka kauracewa jefa kuri'a. Amurka da Isra'ila da wasu kasashe biyu kanana a tekun Pacific sune kawai suka jefa kuri'ar kin yarda da kudurin.

Kudurin na Babban zauren taron MDD ba ya da tasiri kamar na Kwamitin Sulhu, amma kuma yana nuna ra'ayoyin gwamnatocin kasashen duniya kan batun.

Wani babban na hannun damar Malam Arafat ya bayyana kuri'ar a zaman gargadi ga Isra'ila, yayin da jami'an Isra'ila suka ce wannan kuri'ar ihunka-banza ne.

A makon da ya shige majalisar zartaswar tsaro ta Isra'ila ta jefa kuri'ar kawar da shugaban na Falasdinawa, tana mai bayyana shi a zaman mai kawo cikas ga cimma zaman lafiya. Amma kuma majalisar ba ta bayyana lokaci da kuma yadda zata aiwatar da wannan shawara tata ba.

XS
SM
MD
LG