Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Kalilan Suke Samun Muhimmin Maganin Yakar Kanjamau A Afirka - 2003-09-23


Wani sabon rahoto ya ce kashi daya daga cikin dari na mutane miliyan hudu 'yan Afirka dake bukatar wani magani na hana illar da cutar kanjamau take yi wa garkuwar jiki ne kawai suke samun wannan magani.

Kungiyar bayar da agajin kiwon lafiya ta "Doctors Without Borders" ita ce ta gabatar da wannan rahoto da ta rubuta tare da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya jiya litinin, a wurin babban taro na 13 na kasa da kasa kan cutar kanjamau a Afirka da ake yi a Nairobin Kenya.

Ana yin amfani da irin wannan magani mai hana kwayar cuta kyankyashe wasu ruwayen halitta da za su batar da kamanninta ga garkuwar jiki, idan kwayar cutar HIV mai haddasa kanjamau ta fara kai hari kan garkuwar jikin bil Adam, abinda ke sa ko da mura ce tana yin illa sosai ga mutum.

Jama'a suna iya kasancewa dauke da kwayar cutar HIV na tsawon shekaru da dama kafin su bukaci irin wannan magani.

Rahoton ya ja kunnen kasashen Afirka da ko dai su tsara hanyar sayo irin wadannan magunguna masu arha, ko su rika sarrafa kofen magungunan domin jama'arsu.

An ce kashi biyu cikin uku na mutanen dake dauke da kwayar halittar cuta ta HIV suna zaune a kasashen bakar fata na Afirka.

XS
SM
MD
LG