Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Mayar Da Martani Ga Harin Bam Da Aka Kai A Bagadaza - 2003-09-23


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Kofi Annan, ya ce ayyukan da majalisarsa ke gudanarwa a Iraqi za su raunana sosai idan har al'amura suka ci gaba da tabarbarewa a kasar.

Mr. Annan yayi tur da harin bam da aka dana cikin mota jiya litinin a Bagadaza. A wannan harin kunar-bakin-wake da aka kai kusa da hedkwatar MDD an kashe 'yan Iraqi biyu aka raunata wasu 'yan Iraqi fararen hula da 'yan sanda da dama.

Sa'o'i a bayan harin, MDD ta bayar da sanarwar cewa Mr. Annan ya nada tsohon shugaban kasar Finland, Martti Ahtisaari, ya jagoranci wani kwamitin bincike mai zaman kansa wanda zai nazarci matakan tsaro a hedkwatar majalisar a Bagadaza.

A watan da ya shige, an kashe mutane fiye da 20, cikinsu har da babban wakilin MDD a Iraqi, a wani harin kunar-bakin-wake a ofishin majalisar dake Bagadaza.

A halin da ake ciki, babban jami'in Amurka a kasar Iraqi, Paul Bremer, ya ce kasar ba ta shirya sosai domin karbar mulkin kanta ba. Amma kuma ya ce kafa majalisar mulki da aka yi a watan Yuli, wani muhimmin mataki ne na mayar da harkar mulki hannun 'yan Iraqi, amma kuma ba za a mayarwa da kasar cikakken ikon mulkin kanta ba har sai bayan an rubuta sabon tsarin mulki tare da gudanar da zabe.

XS
SM
MD
LG