Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Zata Sako Daruruwan Larabawa Fursunoni, Akasarinsu Falasdinawa... - 2003-09-23


Rahotanni daga birnin al-Qudus sun ce watakila Isra'ila zata sako daruruwan Larabawa fursunoni, akasarinsu Falasdinawa, a wata musanya da kungiyar dakarun sari-ka-noken Hezbollah ta Lebanon.

Rahotannin, wadanda suka ambaci majiyoyin Isra'ila da na Falasdinawa dake da masaniya game da tattaunawar sassan, sun ce watakila musanyar zata kunshi Marwan Barghouti, jami'in Falasdinawa mafi girma da Isra'ila take tsare da shi.

Jamus ce take shiga tsakani a tattaunawar.

Hezbollah tana neman a sako wasu shugabannin 'yan sari-ka-noke su biyu, yayin da Isra'ila take neman a sako wani dan kasuwarta a kuma mika mata gawarwakin sojojinta uku da aka kashe.

A halin da ake ciki, sojojin Isra'ila sun kashe wani dan kungiyar kishin Falasdinu ta Hamas a yankin Yammacin kogin Jordan.

Rundunar sojan Isra'ila ta ce mutumin ya taimaka wajen shirya hare-hare kan 'yan Isra'ila.

XS
SM
MD
LG