Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Tarayya A Nan Amurka Tana Sake Nazarin Hukumci Kan Zaben Kawar Da Gwamnan Jihar California - 2003-09-23


Wata kotun daukaka kara ta tarayya dake Jihar California a nan Amurka tana sake nazarin hukumcin da ta yanke kwanakin baya na jinkirta zaben da aka shirya gudanarwa a wata mai zuwa na kiranye, ko kuma kawar da gwamnan jihar daga kan kujerarsa.

A jiya litinin, alkalai 11 na kotun daukaka kara ta tarayya ta 9 dake zama a birnin San Francisco sun saurari hujjojin masu neman da a jinkirta zaben, da na wadanda ke son a gudanar da shi kamar yadda aka tsara.

A makon da ya shige, wasu alkalai uku na kotun da suka yi zama sun yanke hukumcin cewa zaben da aka shirya gudanarwa ranar 7 ga watan Oktoba domin kawar da gwamna Gray Davis dan jam'iyyar Democrat daga kan kujerarsa tilas a jinkirta shi zuwa gaba saboda injin dake huda katin kuri'a jikin sunan dan takarar da mai zabe yake so, wanda za a yi amfani da shi a kananan hukumomi da yawa, tsohon yayi ne kuma ba ya kirga zahirin yawan kuri'u daidai yadda aka kada.

XS
SM
MD
LG