Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yayi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimaka Wajen Sake Gina Kasar Iraqi - 2003-09-24


Shugaba George W. Bush na Amurka ya roki kasashen duniya da su taimaka wajen sake gina kasar Iraqi, yana mai fadin cewa lokaci yayi na mancewa da bambancen da suka wakana a sanadin farmakin sojan da Amurka ta jagoranci kaiwa kan kasar Iraqi.

Mr. Bush ya bayyana wannan jiya talata a lokacin da yake yin jawabi gaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

Mr. Bush ya shaidawa shugabannin kasashen duniya cewa ya kamata MDD ta taimaka wajen rubutawa Iraqi tsarin mulki, da horas da ma'aikatan gwamnati tare da gudanar da zabe.

Har ila yau ya ce tilas ne a gudanar da wadannan ayyuka bisa bukatun 'yan Iraqi, ba wai a hamzarta su ko kuma a jinkirta ba.

Haka kuma, Mr. Bush yayi kiran da a dauki matakan hana yaduwar makamai masu guba, ko na yada cuta ko kuma na nukiliya. Ya ce 'yan ta'adda suna iya yin amfani da irin wadannan makamai domin haddasa bala'i da bakar wahalar da ko tunaninsa ba za a iya yi ba cikin dan kankanin lokaci.

XS
SM
MD
LG