Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Zata Koma Cikin Kungiyar OPEC A Taronta Na Vienna - 2003-09-24


A yau laraba Iraqi zata koma cikin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC, sai dai kuma ba a san ko zata halarci taron a zaman cikakkiyar wakiliya ce, ko kuma 'yar kallo ba.

Iraqi tana daga cikin kasashen da suka kafa kungiyar OPEC, amma kuma ba ta halarci taron ministocin man kungiyar da aka yi a watan Yuli ba. taron yau laraba shine na farko da Iraqi zata halarta tun bayan hambarar da Saddam Hussein. Sabon ministan manta, Ibrahim Bahral-Uloum shine zai wakilce ta.

Ministan mai na Venezuela, Rafael Ramirez, ya ce bai kamata Iraqi ta halarci taron an Vienna a zaman cikakkiyar wakiliya ba, saboda kasashen duniya ba su amince da halalcin gwamnatinta ba.

Jami'an OPEC sun gana har cikin daren talatar nan, amma kuma sun kasa cimma daidaiton ra'ayi kan matsayin kasar ta Iraqi a wannan taron.

XS
SM
MD
LG