Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakin Iraqi Ya Haddasa Matsaloli Fiye da Wadanda Ya Warware - 2003-09-24


Shugaba Megawati Sukarnoputri ta kasar Indonesiya ta ce yakin da aka yi a Iraqi ya haddasa matsaloli fiye da wadanda ya warware.

Shugabar ta Indonesiya ta shaidawa babban taron MDD cewa Musulmi da yawa suna jin cewa an yi banza da su, yayin da suka yi imani da cewa duk wata manufar hulda da yankin Gabas ta Tsakiya tana nuna fifiko ga kasar bani Isra'ila.

Ta ce wannan, shine yake haddasa tashin hankali da fitina.

Shugaba Megawati ta yi kira ga manyan kasashen duniya du su ringa kamanta adalci, su kuma takali ainihin matsalar dake janyo ta'adanci.

daga baya shugaba Bush ya godewa shugabar ta Indonesiya a saboda yakin da take yi da ta'addanci. Har ila yau ya bayyana Indonesiya a zaman babban misali na kasar Musulmi dake aiki da tsarin dimokuradiyya, kuma abar koyi ga 'yan Iraqi.

XS
SM
MD
LG