Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Liberiya Suna Tilastawa Fararen Hula Yin Aikin Bauta - 2003-09-24


MDD ta bayar da rahoton cewa kungiyoyin 'yan tawaye biyu na kasar Liberiya suna tilasta ma fararen hula yin aikin bauta a yankunan dake hannunsu.

A cikin wani rahoton da ya bayar jiya talata, ofishin yada labarai na MDD, ya ce kungiyar 'yan tawayen arewacin kasar ta "L.U.R.D." tana tilastawa mata girbe shinkafa wa manyan hafsoshin sojan 'yan tawaye daga gonakin dake yankunansu.

Ofishin yada labaran na MDD ya ambaci ofishin Kula da harkokin agajin jinkai na majalisar, OCHA, yana fadin cewa wasu fararen hula a yankin sun mutu a sanadin yunwar da ake fama da ita a dalilin karancin abinci.

Har ila yau, ofishin ya ambaci kungiyoyin agaji suna fadin cewa daya kungiyar 'yan tawayen mai suna "MODEL" ma ta tilastawa fararen hula yin ayyukan bauta a birnin Buchanan mai tashar jiragen ruwa a kudancin kasar.

XS
SM
MD
LG