Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Damfara Yana Cewa Shine Aliyu Mustapha Na Sakkwato - 2003-09-25


Rahotanni daga sassa dabam-dabam na Nijeriya sun bayyana cewa akwai wani dan damfara da yake zagayawa yana fadin cewa shine Aliyu Mustapha Sokoto, ma'aikacin Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Daga Abuja, wakilinmu babangida Jibrin ya ci karo da wasu masu gidan mai da shi wannan dam damfara ya sio ya yaudare su. Amma da suka kira Banagida Jibrin domin ya gana da shi, sai ya gudu.

Haka ma a Ibadan, wannan dan damfara ya yaudari mutane da dama, kafin dubunsa ya cika, amma ya gudu, ba a san inda yake ba.

Daga garin Zing a Jihar Taraba, wani mai sauraronmu mai suna Sa'idu Ibrahim Tela ya aiko mana da takarda ta cin karon da yayi da wannan mutumi, wanda yayi kwanaki yana yaudararsu.

Muna sanar da masu sauraro da su yi hattara da duk wani wanda ya ce shi ma'aikaci ne, to su tabbatar da cewa ya nuna musu katin shaida, har kashi biyu da muke dauke da su. A bayan wadannan katunan shaida guda biyu, muna kuma da katuna dake dauke da sunan kowane ma'aikaci da mukaminsa. Masu sauraro su tabbatar da wadannan.

Haka kuma, muna son ku dubi wadannan hotuna da kyau na Aliyu Mustapha na gaskiya. Duk wani wanda ya zo ya ce shine, kuka ga cewa dan damfara ne, to ku mika shi hannun hukuma.

Kuma ku dubi fuskokin ma'aikatanmu baki daya, ku kasa kunne ku gane muryoyinsu domin maganin 'yan damfara.

Kuma ko da ma'aikacinmu ne, muna rokon jama'a da kada su yarda su ba shi wani abu, domin wannan gidan rediyo yana biyan kudin komai na duk wani ma'aikacin da aka tura aiki.

XS
SM
MD
LG