Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin MDD Ya gamsu Cewa Za A Samu Zaman Lafiya A Sudan - 2003-09-30


Babban jami'in ayyukan agajin jinkai na MDD a kasar sudan ya bayyana kwarin guiwar cewa gwamnati da 'yan tawayen kasar za su cimma zaman lafiya mai dorewa.

Tom Vraalsen ya shaidawa 'yan jarida a hedkwatar MDD a New York cewar a yanzu yana da kwarin guiwa fiye da a kowane lokaci a baya, cewar za a cimma yarjejeniyar zaman lafiyar da zata kawo karshen yakin basasar shekaru 20 a Sudan.

Ya kara da cewa dukkan sassan sun rungumi shirin samar da zaman lafiya, kuma zasu ci gaba da tattaunawa har sai sun cimma zaman lafiya.

A makon da ya shige gwamnatin Sudan da babbar kungiyar 'yan tawayen kasar suka rattaba hannu a kan wata muhimmiyar yarjejeniyar tsaro. An cimma yarjejeniyar bayan tattaunawar kusan makonni uku a tsakanin mataimakin shugaban Sudan, Ali Osman Taha, da madugun 'yan tawayen kungiyar SPLA, John Garang.

XS
SM
MD
LG