Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Wajen Burma Ya Ce Kasarsa Ta Rungumi Aniyar Kafa Mulkin Dimokuradiyya - 2003-09-30


Ministan harkokin wajen Burma ya shaidawa Babban Taron MDD cewar kasarsa ta rungumi aniyar kafa mulkin dimokuradiyya, koda yake har yanzu gwamnati tana ci gaba da takaita kai da komowar shugabar 'yan adawa, Aung San Suu Kyi.

Ministan harkokin waje Win Aung bai ambaci sunan Aung San Suu Kyi cikin jawabinsa na ranar litinin ba, amma kuma ya ce majalisar soja dake mulkin kasar Burma tana da abinda ya kira "kudurin siyasa" na kafa mulkin dimokuradiyya ba tare da hauragiya ba a kasar.

An yi watanni hudu ana tsare da Aung San Suu Kyi a wani wurin da ba a bayyana ba kafin a yi mata tiyata a asibiti. A ranar Jumma'a aka sallame ta daga asibitin, amma ana ci gaba da yi mata daurin talala.

A jiya litinin Amurka ta sake jaddada kiranta na a sako shugabar 'yan adawar ba tare da bata lokaci ba. Wani kakakin ma'aikatar harkokin waje a Washington ya ce a kwanakin baya ma, gwamnatin mulkin soja ta Burma ta toshe yunkurin da jami'an jakadancin Amurka suka yi na ganawa da likitocin shugabar 'yan rajin dimokuradiyyar.

XS
SM
MD
LG