Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Jerin Gwano A Gidajen Mai Na Biranen Nijeriya - 2003-09-30


Dogayen layuka na masu neman man fetur sun komo a gidajen mai na Nijeriya, yayin da jama'a suka fara fargabar cewa gwamnati tana shirin bayyana yin karin farashin mai a wannan kasa.

Shugabannin babbar kungiyar kwadago ta Nijeriya sun ja kunnen shugaba Olusegun Obasanjo da kada ya kuskura yayi karin farashin man, suna masu yin misali da yajin aiki na gama gari da aka yi kwanaki goma ana gudanarwa a farkon shekarar nan kan karin farashin mai na baya.

Gwamnatin Nijeriya ta ce ko ba dade ko ba jima tilas ta yi watsi da shirin yin rangwamen farashin mai, matakin da zai haddasa tashin farashinsa.

XS
SM
MD
LG