Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojan Amurka A Iraqi, Yayin Da Amurka Ta Kama Wadanda Ake Zaton Sun Sace Sojojin Amurka Biyu - 2003-09-30


Jami'an Amurka sun ce hare-haren bam a yamma da birnin Bagadaza sun yi sanadin mutuwar wani sojan Amurka tare da raunata wasu guda uku, yayin da sojojin Amurka suka kama wasu 'yan Iraqi da ake zaton sune suka sace wasu sojojin Amurka biyu a watan Yuni.

Jami'ai sun ce an kashe sojan Amurka guda aka raunata wani jiya litinin, a lokacin da wani bam da aka dasa a gefen hanya ya tashi daidai lokacin da kwambar motocin sojoji ke wucewa a Habbaniya. Irin wannan harin da aka kai a garin Khaldiya dake kusa da nan ya raunata sojoji biyu.

An yi sa'o'i da dama ana gwabza fada a bayan harin na Khaldiya. Shaidu suka ce sojojin Amurka sun mayar da martani tare da taimakon jiragen saman kai farmaki da tankoki da helkwaftoci.

A halin da ake ciki, rundunar sojan Amurka ta ce an kama 'yan Iraqi uku aka kashe na hudu a lokacin da motar da suke tafiya a ciki ta yi kokarin ketawa ta cikin wani shingen da sojojin taron dangi suka yi a kan hanya. Rundunar ta ce a bayan da aka binciki motar, an gano wasu bindigogi biyu na sojojin Amurka guda biyu da suka bace a cikin watan yuni, aka kuma tsinci gawarwakinsu daga baya.

Wadannan al'amura sun wakana a bayan sumamen da 'yan taron dangi suka kai cikin dare a kan wasu gidaje 15 a garin Tikrit inda aka haifi Saddam Husseini.

XS
SM
MD
LG