Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Dake Kula Da Farashin Mai A Nijeriya Ta Ce Gwamnati Ta Janye Rangwame - 2003-10-01


Hukumar dake kula da farashin man fetur da danginsa a Nijeriya ta ce ta janye rangwamen farashin, duk da barazanar da ma'aikata ke yi ta yajin aikin gama gari a kasar.

Wani babban jami'in hukumar ya fada jiya talata cewa daga yanzu 'yan kasuwar dake sayar da man ne za su kayyade farashinsa ba hukumar ba.

Kafofin labarai a Nijeriya sun yi ta buga rahotanni cikin makon nan cewa shugaba Olusegun Obasanjo zai bayar da sanarwar wannan sauyin manufa a jawabin bukin ranar samun 'yancin kai da zai yi a yau laraba.

Wadannan rahotanni sun haddasa fargabar mummunan tashin farashin mai, abinda ya sa aka yi ta samun dogayen layuka a gidajen mai na kasar.

Babbar kungiyar kwadago ta Nijeriya ta yi barazanar kiran yajin aiki na gama gari idan gwamnati ta janye rangwamen farashin man. yajin aikin kwanaki goma da aka yi a bayan karin farashin mai da gwamnati ta yi a farkon shekarar nan ya gurgunta al'amura a kasar har ya kai ga tashe-tashen hankula.

Nijeriya tana daya daga cikin manyan kasashen dake da arzikin man fetur, kuma 'yan Nijeriya suna daukar samun man da arha a zaman hakkinsu.

Sai dai kuma ita gwamnatin ta Obasanjo ta ce tsame hannunta daga harkar farashin mai na daya daga cikin muhimman manufofinta na sauyin tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG