Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubbai Sun Yi Zanga-Zanga A Kasar Ivory Coast - 2003-10-03


Dubban magoya bayan gwamnatin kasar Ivory Coast sun yi zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin yadda 'yan tawaye suke ci gaba da rike rabin yankunan kasar, duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla.

A jiya alhamis 'yan zanga-zangar suka yi dafifi a titunan birnin Abidjan, inda suke neman da 'yan tawaye su ajiye makamansu ba tare da jinkiri ba.

'Yan zanga-zangar sun fito a ranar cikar shekara guda da barkewar tawayen kasar, kuma makonni biyu a bayan da 'yan tawayen suka janye daga cikin gwamnatin karo-karo, abinda ya sa aka fara fargabar sake barkewar fada.

Wata yarjejeniyar zaman lafiyar da Faransa ta shiga tsakani aka kulla a tsakanin sassan a watan Janairu, ita ce ta share fagen kafa gwamnatin ta hadin kan kasa da ta hada da 'yan tawaye.

A jiya alhamis, babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce ya damu sosai da tabarbarewar al'amura a Ivory Coast, ya kuma yi kira ga 'yan tawayen da su koma cikin gwamnati.

XS
SM
MD
LG