Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce Washington za ta ci gaba da kokarin samo hanyar diflomasiyya ta warware rikicin nukiliya na Koriya ta Arewa, duk da sabon ikirarin da hukumomi a birnin Pyongyang suka yi cewar suna karfafa makamansu na nukiliya domin rigakafin kai musu farmakin cin zali.
Mr. Powell ya ce Amurka ba ta da shaidar da zata gaskata wannan ikirari na Koriya ta Arewa.
Koriya ta Arewa ta ce tana yin amfani da makamashin Plutonium da aka kankare daga jikin rodi guda dubu 8 na makamashin nukiliya domin kara yawan makamanta na nukiliya.
Kwararru na Amurka suka ce sun yi imani cewar a yanzu haka ma Koriya ta Arewa tana da makami guda ko kuma guda biyu na nukiliya.
Rodin makamashi guda dubu takwas za su iya samar da makamashin Plutonium na hada makaman nukiliya guda 6.