Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren MDD Yace Bai Gamsu Da Daftarin Kudurin Da Amurka Ta Sake Rubutawa Kan Iraqi Ba - 2003-10-03


Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce daftarin kudurin da Amurka ta sake rubutawa kan Iraqi bai kunshi shawarar da ya bayar ba.

Mr. Annan ya ce sabon daftarin bai kunshi shawarar da ya bayar cewar sojojin Amurka su mayarwa da 'yan Iraqi ikon mulkin kasarsu cikin watanni ba, daga nan kuma su 'yan Iraqin su rubutawa kansu tsarin mulki.

Amurka ta yi gyara ga daftarin kudurin domin maganin korafin ad Faransa da wasu kasashe suka yi cewar za a yi jinkirin mayarwa da 'yan Iraqi mulkin kasarsu. Amma kuma sabon daftarin kudurin na Amurka bai tsayar da lokacin yin hakan ba.

Jakadan Faransa a MDD, Jean Marc de La Sabliere, ya ce kasarsa ba ta gamsu da wannan sabon kudurin ba, saboda har yanzu tanadin da ta yi wa MDD shine na zamowa ta biyu a bayan Amurka wajen kula da harkokin Iraqi.

XS
SM
MD
LG