Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sufeton Makamai Na Amurka Ya Ce Har Yanzu Ba Su Samu Haramtattun Makamai A Kasar Iraqi Ba - 2003-10-03


Babban sufeton makamai na gwamnatin shugaba Bush ta Amurka a kasar Iraqi ya ce har yanu ma'aikatansa ba su samu wani makami ko guda daya na guba a kasar ba.

Sai dai kuma david kay ya ce ba wai wannan yana nufin cewa babu irin wannan makami a kasar ta Iraqi ba ne.

Ya ce har yanzu sufetocinsa suna da aiki mai yawa a gaba kafin su yanke shawara game da makaman kare dangi a Iraqi.

Mr. Kay ya ce ma'aikatansa sun samu kayayyaki da ayyuka masu nasaba da makamai masu guba da na kera makamai masu linzami wadanda Iraqi ba ta fadawa sufetocin makamai na MDD ba.

Mr. Kay yayi magana jiya alhamis a bayan da ya gabatar da rahoton wucin gadi ga kwamitocin kula da ayyukan leken asiri na majalisar dattijai da ta wakilan Amurka game da farautar muggan makaman da suke yi a kasar Iraqi.

XS
SM
MD
LG