Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Son Tsige Gwamna Gray Davis Na Jihar California Suna Raguwa - 2003-10-07


Wata sabuwar kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a ta nuna cewa watakila gwamna Gray Davis na Jihar California zai ci gaba da rike mukaminsa, a yayin da masu jefa kuri'a ke shirin yin tattaki zuwa rumfunan zabe a yau talata domin yanke shawarar ko zasu tsige shi su zabi wani, ko kuma zasu kyale shi ya ci gaba da zama kan wannan gado.

Masu jefa kuri'a zasu kada kuri'u bibbiyu a yau talatar, ta farko a kan ko a cire gwamnan daga kan mukaminsa, ta biyu kuma idan an yarda za a cire shi, a zabi wanda zai maye gurbinsa.

Wata kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a da kamfanin Knight Ridder da NBC News suka gudanar, ta nuna cewa yawan masu jefa kuri'ar da suka ce lallai zasu tsige gwamna Davis ya ragu daga kashi 52 a cikin 100 a makon da ya shige, zuwa kashi 44 daga cikin 100 a ranar asabar.

Wannan kuwa ya biyo bayan zargin da wasu mata su 15 suka yi cewar a cikin 'yan shekarun da suka shige, kuma a lokuta da dama, dan takarar maye gurbin gwamnan, kuma dan jam'iyyar Republican Arnold Swarzeneger ya taba wuraren da bai kamata ba a jikinsu.

Mr. Davis ya ce ya kamata masu gabatar da kararraki su binciki wannan zargi.

Mr. Swarzeneger ya bayyana zargin a zaman wata yaudara ta neman yi masa batunci kawai.

XS
SM
MD
LG