Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsoffin Sojojin Iraqi Sun Yi Zanga-Zanga A Rana Ta Uku - 2003-10-07


Tsoffin sojojin Iraqi sun yi zanga-zanga a rana ta uku suna neman da a biya su albashin da suka yi hasara a bayan da sojojin taron dangi suka wargaza rundunar sojojin kasar.

Tsoffin sojojin sun yi zanga-zanga jiya litinin a biranen kasar Iraqi da dama, suna masu fadin cewa Amurka ba ta biya su dala arba'in-arba'in da ta yi musu alkawari a farkon shekarar nan ba.

An kashe 'yan Iraqi su akalla uku a irin wannan zanga-zanga da aka yi a ranakun asabar da lahadi a biranen Basra da Bagadaza.

A nan Washington, gwamnatin shugaba Bush ta ce tana tsara wani sabon shiri na kawo karshen tashe-tashen hankula a Iraqi da Afghanistan. Kakakin fadar White House ya ce za a kirkiro da wata kungiyar tabbatar da zaman lafiya a Iraqi karkashin jagorancin mai bai wa shugaba Bush shawara kan harkokin tsaron kasa, Condoleeza Rice.

Wannan sanarwa ta zo a daidai lokacin da majalisar zartaswar kasar Turkiyya ta jefa kuri'ar amincewa da tura sojojin kasar domin su shiga cikin rundunar kasa da kasa a Iraqi.

A yau talata ake sa ran cewa majalisar dokokin Turkiyya za ta takali wannan batu.

XS
SM
MD
LG