Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gwamnati Da Na 'Yan Tawayen Liberiya Zasu Kawar Da Dukkan Makamai Daga Monrovia - 2003-10-08


Sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD a Liberiya, sun ce dakarun gwamnati da na 'yan tawaye sun yarda za su kawar da dukkan makamai daga Monrovia, babban birnin kasar, cikin sa'o'i 72, watau kwanaki uku.

Kwamandan rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD, Janar Daniel Opande, ya ce dakarunsa za su fara bincike a fadin birnin domin tabbatar da cewa ana yin aiki da yarjejeniyar. Sassan na Liberiya masu gaba da juna sun yarda za su bayar da hadin kai.

A makon da ya shige, dakarun gwamnati da na 'yan tawaye sun gwabza fada a Monrovia a daidai lokacin da wani madugun 'yan tawaye ya shiga birnin da mota. An kashe mutane akalla uku a dauki-ba-dadin da aka yi.

Wasu mazauna birnin sun dora laifin wannan fada a kan 'yan kiyaye zaman lafiya a saboda ba su kwace makaman 'yan tawayen dake rakiya wa madugunsu, Sekou Conneh, zuwa cikin birnin ba.

XS
SM
MD
LG