Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijeriya Tana Nan Daram Kan Kudurinta Na janye Rangwamen Farashin Mai - 2003-10-08


'Yan majalisar dokokin Nijeriya sun ce gwamnatin tarayya ta tsaya kan bakanta game da janye rangwamen farashin mai, duk da yajin aiki na gama gari da ake shirin farawa daga gobe alhamis.

Mukaddashin shugaban majalisar dattijai, Ibrahim Mantu, ya bayyana cewa gwamnatin ba ta da wani zabi a bayan janye rangwamen.

Gwamnatin shugaba Obasanjo ta janye rangwamen farashin mai haka kwatsam a makon jiya, matakin da ya haddasa tashin farashin man.

Gwamnati ta ce wannan sabuwar manufa zata kawo karshen fasa kwabrin mai tare da tsimin kudin da za a yi amfani da shi wajen gudanar da ayyukan kyautata jin dadin jama'a.

Amma kuma Babbar Kungiyar Kwadago ta Kasar, wadda ta kira wannan yajin aiki, ta ce bai kamata a sanya talaka ya jikkata domin a yi gyara ga tsarin tattalin arzikin kasar ba.

A Abuja, babban birnin Nijeriya, an yi layuka masu tsawon gaske a gidajen mai da bankuna da kantuna saboda tsammanin fara wannan yajin aiki a gobe.

XS
SM
MD
LG