Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Amince Da Tura Sojoji Zuwa Iraqi - 2003-10-08


Majalisar dokokin Turkiyya ta jefa kuri'ar amincewa da tura sojoji zuwa Iraqi, amma wasu 'yan Majalisar Mulkin Iraqi da Amurka ta nada sun ce ba su yarda Turkawa su taka musu kasa ba.

Amurka ta yi marhabin da wannan shawara da Turkiyya ta yanke jiya talata, matakin da zai iya sa a girka sojojin Turkiyya har dubu 10 a Iraqi.

Amma wasu 'yan majalisar mulkin Iraqi sun bayyana adawa da wannan matakin, suna masu fadin cewa girka sojojin Turkiyya zai kara munin halin da ake ciki a Iraqi.

A halin da ake ciki, rundunar sojojin Amurka ta bayar da sanarwa a jiya talata cewar an kashe sojojin Amurka uku da wani tafinta dan Iraqi da maraicen litinin a wasu hare-haren bam biyu a kusa da birnin Bagadaza.

XS
SM
MD
LG