Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidajen Telebijin Na Amurka Sun Ce Arnold Schwarzeneger Ya Zamo Sabon Gwamnan Jihar California - 2003-10-08


Manyan gidajen telebijin na Amurka sun yi hasashen cewa an tsige gwamna Gray Davis na Jihar California a wani zabe na musamman na kiranye da aka gudanar, an kuma zabi gwarzon majigi Arnold Schwarzeneger ya zamo sabon gwamnan jihar.

Har yanzu hukuma ba ta bayar da sakamko ba. Amma kuma sakamakon ra'ayoyin jama'ar da suka jefa kuri'u da aka dauka jim kadan a bayan da aka rufe rumfunan zabe jiya talata, ya nuna cewa jama'a sun tsige gwamna Davis da gagarumin rinjaye. Sakamakon ya kuma nuna cewa masu jefa kuri'a sun zabi wannan gwarzon majigi haifaffen kasar Austria saga cikin 'yan takara fiye da 130 domin ya maye gurbin Mr. Davis.

Watakila za a yi kwanaki da dama ko makonni kafin a samu cikakken sakamakon wannan zabe daga hannun hukuma, a saboda akwai miliyoyin jama'a da suka aika da kuri'unsu ta gidan waya.

Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a na baya-bayan nan sun nuna cewa mafi yawan masu jefa kuri'a sun goyi bayan tsige gwamnan dan jam'iyyar Democrat, kuma da dama suna son maye gurbinsa da Mr. Schwarzeneger dan jam'iyyar Republican.

Yawan masu goyon bayan Mr. Schwarzeneger ya ragu a bayan da wasu mata suka zarge shi da laifin kokarin yin lalata da su cikin shekaru 30 da suka shige. Mr. Schwarzeneger yayi watsi ad zargin a zaman yaudara da neman batunci, koda yake a makon da ya shige ya nemi gafara a saboda nuna hallayan da ba su kamata ba ga mata a can baya.

XS
SM
MD
LG