Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fargabar Mutane 150 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Arewacin Nijeriya - 2003-10-11


Ana fargabar cewa mutane fiye da 150 sun hallaka, a bayn da wani karamin jirgin ruwan jigilar fasinja ya kife ranar alhamis a arewacin Nijeriya.

Wata mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa jirgin yana dauke da mutane fiye da 150, kuma babu wani labarin da aka samu na ceto ko da mutum guda daga ciki. Haka kuma, ba a san ko an tsinci gawar wani a wurin da hatsarin ya faru ba.

Rahotannin dake fitowa daga yankin a yau asabar sun ce wanan jirgin ruwa ya taso ne daga garin Numan a Jihar Adamawa, a kan hanyar zuwa Jen a Jihar Taraba. Jirgin ya ci karo da daya daga cikin kafafun gadar Numan, sai ya kife a wurin.

Wasu rahotanni sun ce a bayan fasinja, jirgin ruwan yana dauke da siminti da wasu kayayyaki.

Ana yawan fuskantar irin wannan lamari a hanyoyin mota da na ruwan Nijeriya. Mutane da yawa suna rasa rayukansu a saboda rashin kyawun jiragen ruwa, ko motoci ko hanyoyi ko kuma dibar kaya da fasinja da ake yi fiye da kima.

An ce ma'aikatan agaji suna can suna ci gaba da kokarin neman ko akwai wadanda har yanzu suna da rai, ko kuma gawarwakin wadanda suka mutu.

XS
SM
MD
LG