Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Zata Binciki Kashe-Kashen Fararen Hula A Kwango-Ta-Kinshasa - 2003-10-14


Ofishin MDD dake Kwango-Ta-Kinshasa ya kaddamar da bincike kan kashe wasu fararen hula su 16 da aka yi a kusa da bakin iyakar kasar da Burundi a farkon watan nan.

Ofishin ya bayar da rahoton cewa wasu mutane su 20 dake magana da harshen Kirundi, harshen da ake amfani da shi wajen harkar gwamnati a Burundi, sun kai farmaki kan mutanen garin Ndunda a ranar 6 ga watan Oktoba.

Akasarin wadanda aka kashe mata ne.

Jami'an MDD suka ce shaidun da suka ga wannan lamari da idanunsu sun shaida musu cewa 'yan tawayen kabilar Hutu na kasar Burundi 'ya'yan wata kungiya mai suna dakarun kare dimokuradiyya sune suka kai wannan farmaki.

MDD ta ce wasu jami'an ofishin nata kuma, suna bin diddigin kashe mutane 65 da aka yi a kusa da garin Bunia dake arewa maso gabashin kasar.

XS
SM
MD
LG