Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Isra'ila Da Falasdinawa Sun Rubuta Yarjejeniyar Zaman Lafiyar Da Babu hannun Gwamnatocinsu A Ciki - 2003-10-14


Wasu 'yan siyasar Isra'ila da na Falasdinawa sun rubuta yarjejeniyar zaman lafiya da nufin kawo karshen gwabza fada a tsakaninsu.

Wadanda suka jagoranci tattauna wannan yarjejeniya sune tsohon ministan shari'ar Isra'ila Yossi Beilin, da wani tsohon ministan Falasdinawa, yasser Abed Rabbo.

An bai wa yarjejeniyar sunan "Yarjejeniyar Geneva" a saboda an tattauna ta a asirce tare da goyon bayan gwamnatin kasar Switzerland. Za a rattaba hannu a kanta nan da 'yan makonni a birnin Geneva.

Nan take gwamnatin Isra'ila ta Ariel Sharon ta yi tur da wannan yarjejeniya, har ma firayim ministan na bani yahudu ya furta cewa 'yan siyasar Isra'ila masu ra'ayin gurguzu ba su da ikon tattaunawa da Falasdinawa.

Ba a bayyana abinda wannan yarjejeniya ta kunsa ba, amma rahotannin kafofin labarai daga Isra'ila sun ce ta tanadi kirkiro da kasar Falasdinu wadda zata kunshi dukkan zirin Gaza da kuma kashi 98 daga cikin 100 na Yankin Yammacin kogin Jordan. Shirin ya kuma tanadi raba birnin Qudus gida biyu, inda unguwannin Larabawa na birnin za su zauna karkashin kasar Falasdinu, su kuma unguwannin yahudawa zasu zauna karkashin Isra'ila.

A wani labarin kuma Falasdinawa shaidu sun ce da asubahin yau talatar nan sojojin Isra'ila tare da tankokin yaki suka shiga sansanin 'yan gudun hijira na Rafah dake bakin iyakar Gaza da Masar.

Majiyoyin sojan Isra'ila sun ce wannan farmaki ci gaba ne da kokarin da suka fara ranar Jumma'a na bincikowa tare da lalata ramukan karkashin kasa da Falasdinawa ke yin amfani da su wajen shiga da makamai.

XS
SM
MD
LG