Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Jakadanci Sun Ce Sabon Kudurin Da Amurka Ta Gabatar Kan Iraqi Ya Tsayar Da Lokacin Tsara Yin Zabe - 2003-10-14


Ma'aikatan jakadanci sun ce Amurka ta fara rarraba daftarin wani sabon kuduri a kan Iraqi ga wakilan Kwamitin Sulhun MDD.

Rahotanni sun ce sabon kudurin zai bai wa Majalisar Mulkin Iraqi wa'adin nan da ranar 15 ga watan Disamba da ta tsara lokutan gudanar da zabe tare da rubuta sabon tsarin mulki.

Wannan daftarin kuduri shine na uku da Amurka ta gabatar tana neman goyon bayan sanya hannun MDD tare da wakilanta a harkokin sake gina iraqi.

Rasha da Faransa da kuma Jamus, wadanda suka yi adawa da yakin da aka yi a Iraqi, sun yi adawa da daftarorin kudurin da Amurka ta gabatar a can baya, suna masu fadin cewa ba za su mayarwa da 'yan Iraqi mulkin kasarsu cikin kankanin lokaci ba.

Amma kuma a jiya litinin, ministan harkokin wajen Jamus, Joschka Fischer, ya ce sabon daftarin ya doshi al-Qibla ta kwarai. Ana sa ran za a jefa kuri'a a kai cikin wannan makon.

XS
SM
MD
LG