Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashi Dan Iraqi Da yayi Hasarar Hannayensa Yace Yana Fata Ba'amurken Da Ya Jefa Musu Bam Shi Ma Zai Sha Irin Wahalar Da Yake Sha - 2003-10-14


Wani yaro dan kasar Iraqi mai suna Ali Abbas, wanda yayi hasarar hannayensa biyu a lokacin da aka jefa bam kan gidansu lokacin yakin ad Amurka ta kai kan Iraqi, ya ce yana fata matukin jirgin saman Amurka da ya jefa musu bam zai sha wahala kamar yadda suka sha.

Ali Abbas mai shekaru 13 da haihuwa, ya shaidawa gidan telebijin na Britaniya a wata hirar da aka yi da shi jiya litinin cewar yana fata matukin jirgin saman "zai kone kamar yadda na kone."

Matashin ya ce bai san abinda 'yan Iraqi suka yi da har za a kai musu hari ba. Har ila yau ya soki Britaniya, yana mai cewa 'yan Britaniya sun yi ta aika masa da wasiku a asibiti yayin da suke taimakawa sojojin Amurka wajen kai farmaki kan kasarsu. An makalawa Ali hannayen roba a wani asibiti na Britaniya.

An kashe mafi yawan 'yan'uwansa a wannan hari da ya lalata gidansu a bagadaza.

An yi ta sanya hotunan wannan yaro da ya kone, kuma ba ya da hannaye, ga shi kuma a firgice a cikin jaridu a fadin duniya.

XS
SM
MD
LG