Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Harba Dan Adam Zuwa Sararin Samaniya - 2003-10-15


China ta harba kumbonta na farko dauke dadan Adam zuwa sararin samaniya, ta zamo kasa ta uku a fadin duniya da ta taba aikewa da dan Adam domin yin shawagi a samaniya.

Kamfanin dillancin labaran China na Xinhua ya ce a yau laraba da asubahi, watau da karfe 2 na dare agogon Nijeriya, aka harba wannan kumbo mai suna "Shenzhou -Five" daga hamadar Gobi dake arewa maso yammacin China.

Kumbon yana dauke da dan sama jannatin China na farko, Yang Liwei, mai shekaru 38 da haihuwa kuma matukin jirgin saman yaki.

Gidan telebijin na China ya ce kumbon ya kai daidai inda aka shirya zai fara yin shawagi yana kewaya duniya. An shirya cewa kumbon zai kewaya duniya sau 14 kafin ya sauko a yankin tsakiyar Mongolia.

Kafofin labaran China suka ce kumbon zai yi wannan shawagi cikin sa'o'i 20.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ambaci dan sama jannatin Kanar Yang yana fadin cewa yana jin garau a bayan da aka harba shi. Har ila yau, kamfanin dillancin labaran ya ambaci shugaba Hu Jintao yana fadin cewa harba wannan kumbo abin tarihi ne ga al’ummar China.

Wannan harba kumbo da China ta yi, ya zo shekaru 42 a bayan da Tarayyar Soviet ta zamo kasar farko da ta fara harba kumbo dauke da dan Adam zuwa sararin samaniya. Makonni uku bayan wannan Amurka ta bi sawunta.

XS
SM
MD
LG