Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Sun Ce Za A Iya Ceton Rayukan Yara Akalla Rabin Miliyan A Kowace Shekara - 2003-10-17


Kwararru kan ayyukan kiwon lafiya na kasa da kasa sun ce a kowace shekara, za a iya ceton rayukan yara dubu 500 idan har za a yi musu allurar rigakafin kamuwa da cutar kyanda wadda ana iya hana kamuwa da ita.

Wakilai daga kasashe 60 suna ganawa a Cape Town a Afirka ta Kudu cikin wannan mako domin auna kamun ludayin yaki da wannan cuta a duniya. Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya da kuma Asusun Tallafawa Yara na MDD sune suka shirya wannan taro.

A bara, Taro na musamman kan yara da babban zauren shawarwarin MDD ya gudanar ya ajiye shekarar 2005 ta zamo shekarar da za a rage yawan yara dake mutuwa daga cutar kyanda da rabi idan an kwatanta da adadin shekarar 1999. Dabarar da aka tsara ita ce ta rage mutuwa a sanadin cutar kyanda ta hanyar yin allurar rigakafi wa jarirai da yaran da suka fara girma tare da bullo da hanyar gano bullar annobar cutar cikin gaggawa tare da daukar matakan murkushe ta.

Kwararru suka ce a kowace rana ta Allah, yara dubu biyu suke mutuwa a fadin duniya a saboda ba a yi musu allurar rigakafin kamuwa da wannan cuta ba. Kashi 95 daga cikin 100 na masu kamuwa da cutar kuwa suna nahiyar Afirka ne.

XS
SM
MD
LG