Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun MDD Ya Amince Da Kuduri Kan Iraqi Ba Tare Da Hamayya Ba - 2003-10-17


Kwamitin Sulhun MDD ya amince ba tare da hamayya ba, da kudurin da Amurka ta gabatar domin neman gudumawar sojojin kasashen duniya tare da kudi domin maido da kwanciyar hankali a Iraqi.

Shugaba Bush yayi marhabin da kuri'ar ta jiya alhamis, yana mai fadin cewa wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da 'yanci a Iraqi. Sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell, ya ce kudurin ya samar da wani izni na MDD da zai iya taimakawa Amurka wajen shawo kan sauran kasashe da su tura sojojinsu su kuma bayar da kudi.

Wannan kuri'a dai nasara ce ta fuskar diflomasiyya ga Amurka da Britaniya. Amma kuma, Jamus da Faransa da kuma Rasha, wadanda tun farko suka yi adawa da kudurin, sun ce ba za su bayar da ko sisin kwabo ba, haka kuma ba za su tura sojojinsu domin tallafawa rundunar taron dangin da Amurka take yi wa jagoranci a Iraqi ba.

A halin da ake ciki, sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya ce Amurka tana tattaunawa da kasashe biyar ko shida kan batun shiga cikin wata rundunar soja ta kasa da kasa a Iraqi. Amma kuma ya ce ba a san ko kasashen za su yarda su shiga ciki ba, ko kuma a wani lokaci za su yi haka.

Mr. Rumsfeld ya ce kara sojoji daga Turkiyya ko wasu kasashen zai dauki lokaci a saboda sai kwamandojin sojan Amurka da 'yan majalisar Mulkin Iraqi sun cimma yarda a kan yadda za a girka sojojin. Pakistan dai ta ce ba za ta tura sojojinta ba.

XS
SM
MD
LG