Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Yayi Kira Ga Morocco Da Ta Amince Da Shirin Zaman Lafiya Na MDD A Yankin Yammacin Sahara - 2003-10-21


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, ya roki Morocco da ta amince da shirin samar da zaman lafiya a Yankin Yammacin Sahara wanda majalisar ta zana kafin karshen shekarar nan.

Mr. Annan yayi rokon da a amince da wannan shirin da aka zana domin kawo karshen rikicin shekaru 28 da ake yi a kan wannan yanki na Yammacin Sahara.

Morocco tana ikirarin mallakar Yammacin Sahara, yayin da kungiyar dakarun POLISARIO take gwagwarmayar ganin yankin ya samu 'yanci.

Wannan shirin samar da zaman lafiya, wanda wakilin MDD na musamman, James Baker, ya zana, ya tanadi bai wa yankin ikon cin gashin kai na wucin gadi, daga baya kuma a gudanar da kuri'ar raba gardama a kan makomar wannan yanki.

XS
SM
MD
LG