Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren NATO Yace Gina Hedkwatar Soja Ta Tarayyar Turai Bata Kudi Ne Kawai - 2003-10-22


Babban sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO, George Robertson, ya bayyana shirye-shiryen gina hedkwatar ayyukan soja ta kasashen Tarayyar Turai a zaman aikin bata kudi kawai.

Mr. Robertson ya bayyana wannan a bayan da manyan jami'an jakadanci suka gana a birnin Brussels, domin tattauna wannan shirin da ake cacar-baki kai, wanda kasashen Belgium da Faransa da Jamus da kuma Luxembourg suka gabatar.

Mr. Robertson ya ce ya kamata kasashen Tarayyar Turai su zuba dukiyarsu wajen samar da abubuwan da ake matukar bukata ba wai su barnatar da kudi wajen kera gine-gine da kuma kayayyakin da NATO tana da su a yanzu haka ba.

Babban jami'in hulda da kasashen waje na Kungiyar Tarayyar Turai, Javier Solana, ya ce dukkan kungiyoyin biyu sun amince kan bukatar kaucewa kofen abinda waninsu ke da shi.

Amma kuma ya ce tilas ne Tarayyar Turai ta zauna da shirin gudanar da ayyuka kamar irin wanda aka gudanar kwanakin baya a kasar Kwango-ta-Kinshasa, aikin da babu hannun kungiyar NATO a ciki.

Amurka tana yin adawa sosai da matakin gina hedkwatar soja ta tarayyar Turai dabam da ta NATO.

XS
SM
MD
LG