Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Zai Ziyarci Bali Domin Nuna Goyon Baya Ga Gwagwarmaya Da Ta'addanci - 2003-10-22


Shugaba George Bush na Amurka ya isa tsibirin Bali domin ziyarar nuna goyon baya ga gwagwarmayar da kasar Indonesiya take yi da ta'addanci.

An takaita ziyarar ta Mr. Bush ga sa'o'i uku a filin jirgin saman tsibirin kawai a saboda damuwa kan sha'anin tsaron lafiyarsa. A farkon wannan makon, hukumomin Indonesiya sun yi kashedin cewa watakila ana dab da kai hare-haren ta'addanci a kasar.

An shirya Mr. Bush zai gana da shugabannin Musulmi masu sassaucin ra'ayi da kuma shugaba Megawati Sukarnoputri domin yabawa kokarinta na yaki da ta'addanci.

Wannan ziyara ta shugaban Amurka ta zo shekara guda a bayan da 'yan harin bam na kunar-bakin-wake suka kashe mutane 202 a wasu gidajen rawa guda biyu na Bali. Ziyarar ta yau laraba zata zamo rangadi na biyar da Mr. Bush zai yada a ziyarar kasashe 6 na Asiya da yake yi, wadda kuma zai kammala gobe alhamis a kasar australiya.

XS
SM
MD
LG