Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Yi Watsi Da Tayin Da Amurka Ta Gabatar Mata Na Tabbacin Tsaro - 2003-10-22


Koriya ta Arewa ta sanya kafa ta shure tayin Amurka na ba ta tabbacin tsaro daga kasashe da dama domin ta watsar da shirinta na kera makaman nukiliya.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa ya watsa wani sharhi da maraicen jiya talata, yana mai cewa tayin "abin dariya ne" kuma "bai ma kamata a nazarce shi ba." Sharhin ya sake nanata bukatar cewa lallai Amurka ta sanya hannu kan yarjejeniyar cewa ba za ta kai farmaki ma kasar ba.

Gwamnatin shugaba Bush ta sha kin yarda da bukatar sanya hannu kan yarjejeniyar cewa ba za ta kai wa kasar farmaki ba.

Amma a farkon wannan makon, shugaba Bush ya ce akwai damar bai wa Koriya ta Arewa wani irin tabbaci na tsaro tare da hadin kan sauran shugabannin kasashen yankin.

XS
SM
MD
LG