Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za A Bude Taron Kasashen Duniya Masu Bayar Da Agaji Kan Kasar Iraqi - 2003-10-23


A yayin da ake dab da bude taron kasashen duniya masu bayar da agaji kan kasar Iraqi a yau alhamis a kasar Spain, jami'an Amurka suna nazarin tsare-tsaren da ake da su na tura kudaden agajin da za a tara ga shirin sake gina kasa na Iraqi. Wakiliyar Muryar Amurka, Laurie Kassman, ta ce Babban Bankin Duniya yayi kiyasin cewa za a bukaci kimanin dala miliyan dubu 36 domin sake gina kasar Iraqi. A bayan wannan kuma, za a bukai karin dala miliyan dubu 19 domin maido da ayyukan tono man fetur da na tsaro.

Kasashe da dama, da kuma kungiyoyi na kasa da kasa, za su fara ganawa yau alhamis a birnin Madrid a kasar Spain domin ganin ko nawa za su iya tarawa daga cikin wannan kudi da ake bukata. A yayin da ake sa ran Amurka zata samar da kudi fiye da dala miliyan dubu 20 kai tsaye na agaji ga ayyukan sake gina kasa da ta tsara a Iraqi, an kafa asusu dabam domin saka kudaden agaji daga wasu kasashen da kungiyoyi. Shugaban Hukumar bayar da Agajin Raya Kasashe Masu Tasowa ta Amurka, Andrew Natsios, ya ce wannan zai bai wa kananan kasashe saukin bayar da gudumawa.

Mr. Natsios ya ce, "Ka san kananan kasashe masu mutane miliyan hudu ko biyar dake son bayar da gudumawa ba su da mutane a can Iraqi wadanda za su iya gudanar da ayyukan da suke a gudanar da kudadensu na agajin. Ba su iya gudanar da ayyuka a kasashe masu tasowa, kuma ba su da sukunin yin hakan. A saboda haka aka bayar da sanarwar kafa wannan asusun tallafi tare da wasu guda biyu da bankin duniya tare da Hukumar Raya Kasashe ta MDD suke gudanarwa domin amfanin wadannan kasashen da ba su son tura mutanensu zuwa Iraqi domin gudanar da ayyuka..."

Karamin sakataren baitulmalin Amurka mai kula da harkokin kasa da kasa, John Taylor, ya ce wadannan asusu da aka kafa ba zai hanawa kasashen duniya kulla yarjejeniyar tallafawa kai tsaye a tsakaninsu da kasar Iraqi ba. Mr. Taylor ya kara da cewa, "Kasashe da dama za su taimakawa Iraqi kai tsaye ta hannun hukumominsu na hadin guiwa kamar yadda suka taimakawa wasu kasashe ta wannan hanya a can baya. Wannan wani zabi ne. Kowace kasa da irin hanyar da ta fi dace mata wajen bayar da agaji. Kuma muna son mu kwadaitawa kasashe ta hanyar samar da hanyoyin da suka fi dace musu, ya Allah ko suna son su yi amfani da kungiyoyinsu na agaji ko suna son yin aiki da ka’idojinsu na bayar da kwangilar ayyukan agaji, ko kuma sun fi son yin amfani da asusun da aka kafa."

Japan da Britaniya da Spain sun yi alkawarin bayar da dubban miliyoyin daloli. Amma kuma ya zuwa yanzu, Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin bayar da dala miliyan 230 ne kawai, kudin da ta bayyana a zaman wanda ya dace a saboda yanayin tsaron da ake fama da shi yanzu haka a Iraqi. Karamin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin tattalin arziki, kasuwanci da aikin gona, Al Larsen, ya ce yana sa ran KTT zata bayar da karin agaji nan gaba, yana mai cewa "Mun sha jin suna nanata cewar tilas ne a samu nasarar aikin sake gina kasar Iraqi, cewar yana da matukar muhimmanci ga muradun gwamnatocin kasashen Turai a samu nasara. Muna fata cewar gudumawar da turai zata bayar nan gaba zai dace da muradun da suka bayyana na tabbatar da nasarar aikin sake gina kasar Iraqi."

Har ila yau, Mr. Larsen ya ce yana sa ran su ma kasashen larabawa za su bayar da gudumawa, domin a cewarsa "...Wadannan (kasashe na Larabawa) sune kasashen da suka fi fuskantar barazana daga Saddam Hussein. Sune zasu fi cin moriya idan Iraqi ta zamo mai arziki da bin tafarkin dimokuradiyya. Sune zasu ji jiki idan Iraqi ta abka cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali ko kuma ta sake kunno kai a zaman mai yin barazana ga makwabtanta. A saboda haka muna tsammanin za su bayar da gudumawa mai tsoka da zai yi la’akari da muradinsu na ganin an samu nasarar aikin sake gina kasar Iraqi."

Kasashe da dama sun bayyana dari darin taimakawa wajen biyan kudin sake farfado da kasar Iraqi har sai sojojin mamaya na Amurka sun mayar da mulkin kasar hannun 'yan Iraqi.

XS
SM
MD
LG