Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Sufeto-Janar Na 'Yan Sandan Kasar Ivory Coast - 2003-10-24


Gwamnatin Ivory Coast ta kori babban baturen 'yan sanda na kasar, kwanaki biyu a bayan da wani dan sanda ya bindige ya kashe wani dan jarida Bafaranshe.

Wata sanarwar da gwamnati ta bayar a Abidjan, ta ce an yanke shawarar korar janar Adolphe Baby ne a lokacin wani taron majalisar zartaswar kasar da aka gudanar karkashin jagorancin shugaba Laurent Gbagbo.

Wani dan sanda ya harbi Jean Helene, wakilin gidan rediyon kasa da kasa na Faransa mai suna "Radio France International" a kai, a bayan wani musu a kusa da hedkwatar 'yan sanda. Mr. Helene yana jira ne domin yayi hira da wasu 'yan adawa da za a sako daga wakafi a lokacin.

A jiya alhamis an dauki gawar Mr. Helene zuwa birnin Paris domin yi masa jana'iza.

Shugaba Jacques Chirac yayi tur da kashe dan jaridan, yana mai dora laifi a kan wasu hukumomin Ivory Coast da bai bayyana ba wadanda ya ce sun haddasa yanayin zaman gaba.

Shugaba Gbagbo yayi alkawarin gudanar da cikakken bincike, yana mai bayyana kashe Mr. Helene a zaman kisa na rashin imani.

Shugaba Gnassingbe Eyadema na Togo ya bayyana kisan a zaman mummunan cin zarafin akidar 'yancin fadin albarkacin baki da dimokuradiyya a kasar Ivory Coast. Kungiyar 'yan jarida ta kasar Ivory Coast ta bayyana kashe Mr. Helene a zaman aikin keta da ya bata sunan kasar.

Magoya bayan shugaba Gbagbo suna zargin 'yan jaridun kasashen waje dake Ivory Coast da laifin nuna son kai ga 'yan tawayen da suka kaddamar da mummunar tayar da kayar baya a bara.

XS
SM
MD
LG