Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Concorde Yayi Jigilar Fasinja Na Karshe - 2003-10-24


Jirgin saman nan mai saurin tafiya da ake kira "Concorde" yayi jigilar fasinja na karshe a lokacin da ya sauka a birnin New York, sa'o'i uku da rabi kawai bayan tasowarsa daga London.

Jirgin na kamfanin safarar jiragen saman British Airways ya sauka jiya alhamis a babban filin jiragen sama na Kennedy dake New York dauke da fasinjoji na karshe da suka biya kudin wannan tafiya.

A yau Jumma'a kuma, jirgin na Concorde zai tashi domin yin tafiyarsa ta karshe a lokacin da zai dauki baki da wadanda suka lashe gasar yin tafiya ta karshe cikin jirgin zuwa filin jiragen saman Heathrow a London.

Kamfanin British Airways zai daina aiki da jiragen masu tsananin gudu a bayan shekaru 27 suna tsallaka tekun Atlantika. daya kamfanin dake amfani da irin wadannan jirage, Air france, ya daina amfani da su a cikin watan Mayu.

Kamfanonin safarar jiragen saman sun koka da cewa ba su samun isassun fasinjoji dake biyan kudi mai tsada na yin tafiya cikin wannan jirgi mai kujerun alatu kawai.

XS
SM
MD
LG