Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Yayi Rokon Da A Bayar Da Gudumawa Mai Tsoka Ga Iraqi - 2003-10-24


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, yayi roko ga kasashe masu bayar da agaji da su bayar da gudumawa mai tsoka ga aikin sake gina kasar Iraqi, yana mai cewa ba za a iya dakatar da aikin har sai mulki ya koma hannun gwamnati ta 'yan kasar ba.

Mr. Annan ya shaidawa taron kasashe masu bayar da agaji na duniya da aka bude jiya alhamis a Madrid cewa Iraqi tana bukatar agajin gaggawa a yanzu. Ya kara da cewa ba za a iya dakatar da aikin sake gina kasa har sai an kyautata tsaro, tare da fara daukar matakan siyasa na mayar da mulki hannun 'yan Iraqi ba.

Ba a dai tsayar da abinda ake bukata a wannan taron kwanaki biyu ba, amma kuma wani rahoto na MDD da Bankin Duniya ya ce Iraqi zata bukaci kudi fiye da dala miliyan dubu 36 domin ayyukan samar da kayayyakin bukatu cikin shekaru hudu masu zuwa.

A halin da ake ciki, leftana-janar Norton Schwartz na rundunar sojojin Amurka ya ce kungiyar Ansar-al-Islam ta Iraqi mai tsattsauran ra'ayi ita ce babbar barazana ga sojojin Amurka a Iraqi. A farkon shekarar nan sojojin Amurka suka lalata hedkwatar kungiyar.

A tashin hankali jiya alhamis kuma, an kashe sojan Amurka guda aka raunata wasu biyu a harin bam a arewa da birnin Bagadaza. An raunata wani sojan guda a garin Fallujah dake yamma da Bagadaza a harin da aka kai kan sojojin Amurka a rana ta biyar a jere a wannan garin.

XS
SM
MD
LG